Thursday, July 18
Shadow

Mutane 30 Sun Mutu An Kwantar Da Wasu Gommai a Asibiti Bayan Sun Sha Burkutu a India

Mutane 30 Sun Mutu An Kwantar Da Wasu Gommai a Asibiti Bayan Sun Sha Burkutu a India

Aƙalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su inda kuma aka kwantar da gommai a asibiti bayan da suka sha wata giya haɗin gida a gundumar Kallakuruchi da ke jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya.

Hukumomin Kasar sun ce yawancin waɗanda aka kwantar a asibitin sama da 80 suna fama ne da amai da gudawa da kuma ciwon ciki bayan sun sha giyar ta burkutu a ranar Talata da daddare.

An kama jami’ai goma da suka haɗa da wani babban jami’in haraji da Baturen ƴan sanda a kan afkuwar lamarin.

Karanta Wannan  Bidiyo: Tinubu da 'yan majalisa suna rera sabon taken Najeriya

Babban minista na jihar ta Tamil Nadu, MK Stalin ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara cewa lamarin ya girgiza shi matuka.

Ministan ya kuma sanar da diyyar dala dubu 12 ga iyalan waɗanda suka mutu, su kuwa waɗanda aka kwantar a asibiti za a ba kowane mutum ɗaya dala 600.

Kowacce shekara gomman mutane suna mutuwa a Indiya sakamakon shan giyar da ake yi ta gargajiya, inda yawanci ake sanya mata sinadarai da suka wuce kima.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *