Mutane 30,000 ne suka je neman aikin da za’a dauki mutum 1,100 a kasar Pakistan.
‘Yansandan kasar ta Pakitan sun kasa iya kula da yawan jama’ar dake neman aikin saboda yanda suka cika babban filin wasa na kasar.
Mutanen sun tarune dan rubuta jarabawar neman shiga aikin.
Rashin aikin yi yayi yawa a kasar ta Pakistan inda rahotanni ke nuna cewa kaso 3 na matasan kasar basu da aikin yi