Kididdiga ta nuna cewa, mutane akalla 3,586 ne ‘yan Bindiga suka kashe a tsakanin watannin Janairu zuwa Maris na shekarar 2022 da suka gabata.
Kamfanin Beacon Consult data ne ya bayyana haka, kamar yanda babban lauya, Bulama Bukarti ya ruwaito.
Yace idan haka ta ci gaba, nan da karshen shekarar 2022, za’a kashe mutane kusan 14,000 a Najeriya.
Ya kara da cewa, a shekarar 2015 lokacin da Kungiyar Boko Haram ta zama kungiyar da ta fi kashe mutane da yawa, mutane 6000 ne aka kashe.
In Q1 of 2022 (Jan-Mar), terrorists killed 3,586 Nigerians according Beacon Consulting data. If this trend continued till the end of the year, >14000 people would be killed. In 2015 when Boko Haram became world’s deadliest terror group, it killed 6,000. It’s never been this ugly!
https://twitter.com/bulamabukarti/status/1515285498184540162?t=3vjqaqLa2GOT7jQC9csWjQ&s=19