Jihar Kogi ta tabbatar da cewa kimanin mutane 41 ne suka kamu da cutar zazzabin lassa, kuma bakwai sun rasa rayukansu tun watan janairu.
Sakataren ma’aikatar kiwon lafiya ne ya tabbatar hakan a wata wasika a birin Lokoja, Mr. Daniel Alonge.
Inda ya kara da cewa gwamna Yahaya Bello yana iya bakin kokarin shi akan annobar domin ya bayar da kudi a yake cutar.