fbpx
Friday, July 1
Shadow

Mutane 6900 sun kamu da kwayar cutar kanjamau a tsakanin watan janairu zuwa yuni a jihar Oyo

Hukumar kula da yaki da cutar kanjamau ta jihar Oyo (OYSACA) ta sanar da cewa tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2020, sama da mutane 6,900 ne suka kamu da cutar kanjamau a Jihar duk da matakan da aka dauka na takaita yaduwar cutar.

A yayin da take gabatar da jawabi ga manema labarai ranar Alhamis don fara bikin shekara ta 2020 na cutar kanjamau a Ibadan, Shugabar kungiyar OYSACA kuma matar Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Tamunomini Makinde, ta ce yaduwar kwayar cutar ta HIV a jihar ta ci gaba zuwa kashi 0.9 cikin dari, tare da karin mata a matsayin wadanda aka suka fi kamuwa fiye da maza.
Injiniya Makinde wandda ta samu wakilcin babban sakatariyar OYSACA, Dakta Lanre Abass ta sanar da cewa ya zuwa watan Yunin 2020, hukumar ta bada shawarwari tare da gwada sama da mutane 765,000, tare da kashi 0.9 cikin 100 na wadanda suka kamu duk da cewa jihar ta sayi kwaroron roba na Naira miliyan 4 don rarrabawa a cikin al’umma a zaman wani bangare na matakan dakile yaduwar cutar kanjamau.
Ta kara da cewa daga cikin uwaye 230,000 da aka ma gwaji, 690 da aka gwada sun kamu da ita duk da cewa a halin yanzu marasa lafiya 21,452 na karbar magani na kanjamau a jihar Oyo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.