fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Mutane 7000 na kira ga kasashen Tutai su hana Gwamna El-Rufai shiga kasashensu

Yayin da ake tsaka da Rahotannin dake nuna cewa kasar Amurka ta saka gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai cikin ‘yan Najeriya da ta hana shiga kasarta, wasu ‘yan Najeriya 7000 sun sakawa wani kira hannu dake neman kasashen Turai suma su hana gwamnan zuwa kasashensu.

 

Tsohon hadimin tsohon shugban kasa, Reno Omokri ne ya fara wannan kiraye a shafin Change.org inda ya bayar da dalilan cewa a baya gwamna El-Rufai ya baiwa ‘yan ta’adda kudi dan su daina kaiwa mutane hari, abinda ya zuzuta wutar rikicin dake faruwa a Kaduna.

Karanta wannan  Don Allah ka dauki mace a matsayin abokiyar takararka, matan APC suka roki Tinubu

Hakanan ya kuma zargi da kai wani Fasto dake Zaria kotu saboda zargin bata masa suna, Omokri ya kuma zargi El-Rufai da yiwa kasashen Turai barazana a lokacin zaben shekarar 2019 wanda yace da wadannan dalilai ne yake neman kasashen Turai da su bi sahun kasashen Amurka wajan hana Gwamna El-Rufai shiga kasashensu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.