Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa Coronavirus/COVID-19 ta dawo gadan-gadan inda kuma tuni wasu jihohi suka fara daukar matakin dakile cutar na sake kulle guraren tarukan jama’a.
Gwamnatin tarayya ma ta yi gargadin cewa a kiyayen bin dokar ta Coronavirus/COVID-19 dan gujewa sake saka wani kulle.
A wannan karin cutar ta Coronavirus/COVID-19 ta fi kama mutane fiye da baya inda a rana daya an samu ta kama mutane fiye da Dubu 1.
Da yake martani akan dawowar cutar, Jigo a Siyasar Jihar Kaduna kuma Uban kasa, Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa a yanzu ne za’a ga illar rashin yarda tsakanin shuwagabannin da Jama’a.
Yace mutane ba zasu yadda su bi matakan da shuwagabannin zasu dauka ba saboda dawowar Coronavirus/COVID-19, domin an shasu sun warke. Ba zasu bi ka’idojin da ake cewa a biba, Subhanallah.
Ya bayyana hakane ta shafinsa na zumunta.
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2926809680885625&id=100006698646237