Mutane bakwai cikin wa’yanda ‘yan bindiga sukayi garkuwa dasu a jirgin kasa na jihar Kaduna da suka kaiwa hari sun samu ‘yanci.
Hadimin Sheik Ahmad Gumi wanda ya kasance daya daga cikin mutanen dake sasantawa da ‘yan bindigar, Malam Tukur Mamu ne ya bayyana hakan ranar asabar.
Inda yace sasantawa ce da sukayi ta fahimta tasa suka sako mutanen guda bakwai wanda a cikin su hadda yaro shugaban kungiyar dattawan Arewa, farfesa Ango Abdullahi.