A ranar Laraba ne mutane biyar da suka hada da mata uku suka kone kurmus a wani hatsarin da ya afku a hanyar Awka zuwa Enugu a jihar Anambra.
Hadarin wanda ya afku a Nawfia da misalin karfe 6:30 na safe, ya hada da motoci biyu, Toyota Highlander da Hiace Bus dauke da mutane biyar.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa direban bas din yana bayan Highlander ne sai kwatsam ya rasa yadda zai yi a lokacin da yake kan gudu, inda ya kutsa cikin motar.
Rahotanni sun bayyana cewa motocin biyu sun kama da wuta nan take.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Adeoye Irelewuyi, ya danganta hatsarin da gudu fitar hankali.
Ya ce jami’an hukumar kashe gobara ta jihar ne suka kashe gobarar.
Ya jajantawa iyalan mamatan, inda ya gargadi masu ababen hawa a jihar da su guji yin gudu sosai tare da tabbatar sun bi ƙa’idodi tuki.