fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Mutane biyu sun mutu, takwas sun jikkata a wani hatsarin motoci a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja

An tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu takwas suka samu munanan raunuka bayan hadarurruka da dama kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Hadarin ya faru ne bayan da motocin da ke taho da gudu suka fada cikin motoci masu zuwa ta gaban su.
Wata sanarwa daga Kwamishinan, Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa hatsarin wanda ya afku a kusa da gonar Olam ya shafi motoci hudu kamar yadda jami’an tsaron da ke gudanar da aiki suka ruwaito.
Jami’an tsaron sun bayar da rahoton cewa, hatsarin ya afku ne sakamakon saurin gudu da tukin kan hannnun da bana su ba.
Sanarwar ta sanar da cewa rashin kwuccewar motar ya haifar da hadarurruka da dama da suka hada da motocin guda hudu wadanda duk suka kauce hanya cikin hadari.
A cewar sanarwar, hukumomin tsaro sun amsa kiran gaggawa sannan suka kwashe wadanda suka rasa rayukansu tare da ba da kulawa ta gaggawa ga wasu mutum takwas da suka jikkata.
Sanarwar ta ce wasu daga cikin wadanda suka jikkata ba su cikin hayyacinsu amma an kai su asibiti yayin da hukumomin tsaro suka share wurin kuma suka taimaka wajen tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda aka saba.
Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya nuna bakin ciki a kan rahoton kuma ya jajantawa dangin mamatan tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun sauki.
Ya nuna kaduwarsa kan yawaitar karya dokar hanya sannan ya sake yin kira ga direbobin da ke bin babbar hanyar don su guji mummunar dabi’ar tuki ta hannun da bana su ba.
Ya kara da jan kunnen hukumomin tsaro da su dage sosai wajen aiwatar da dukkan abubuwan da Gwamnatin Kaduna ta hana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Mutane 18 sun mutu sakamakon hadarin mota akan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

Leave a Reply

Your email address will not be published.