fbpx
Monday, October 26
Shadow

Mutane Biyu Sun Rasu Bayan Da Wani Gini Ya Rushe a Jihar Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto mutane 10 da suka makale a wani gini da ya rushe a Gwammaja ‘Yan Kosai da ke karamar hukumar Dala ta jihar.

Malam Saidu Muhammed, mai magana da yawun ma’aikatan, ya fadi haka ne a wata sanarwa a ranar Talata a Kano.
“Mun samu kiran waya ne da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Talata daga wani mai suna Malam Abdullahi Muhammad.
“Da samun labarin, sai muka hanzarta tura jami’anmu na ceto zuwa wurin da misalin karfe 1:37 na safe.
“Mun gano cewa gidan, gini mai hawa daya, ya fada kan mazauna 10 kuma an rufe su da karyayyun bulo da yashi,” in ji Muhammad.
Ya ce mutum takwas daga cikin 10 da ke cikin ginin an kubutar da su da rai kuma an kai su asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Kano don kula da lafiya, yayin da sauran biyu aka samu sun mutu kuma an kwashe gawarwakinsu zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa sun mutu.
Ya shawarci mazauna jihar da su kula da muhallinsu kuma su guji zama a cikin gine-ginen da suka tsage.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *