Saturday, April 4
Shadow

Mutane Biyu Sun Sake Kamuwa Da Cutar Corona Virus A Jihar Bauchi

An tabbatar da mutum biyu da suka yi mu’amula da gwamnan Bauchi Bala Mohammed sun kamu da cutar corona virus a jihar Bauchi.

 

 

Kwamishinan Lafiya na jihar Bauchi Dr. Aliyu Maigoro, shi ne ya bayyana wa manema labarai lamarin a yau Alhamis.

 

 

Za a iya tuna cewa tuni gwamnatin jihar ta bayyana cewa, an gwada an kuma tabbatar da gwamnan jihar na dauke da cutar coronavirus, sannan kuma an killice mutum 27 har sai sun yi kwanaki 14 domin tabbatar da suna dauke da cutar ko rashin ta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *