Tauraron dan kwallon kafar Najeriya, Ahmed Musa ya musanta masu ce masa tsoho.
Musa yayi wannan maganane a Legas ranar Juma’a a wajan taron masu ruwa da tsaki kan harkar kwallon kafa.
Yace da yawa na cewa Musa ya tsufa, amma maganar gaskiya ni ba tsoho bane.
Yace tun yana da shekaru 19 yake bugawa Super Eagle wasa shiyasa da yawa ke ganin ya tsufa saboda dadewarsa a kungiyar.
Yace yana jin dadi da Alfahari idan ya saka rigar kwallon Najeriya.
A rahoton da jaridar Punchng ta ruwaito, Musa yace yana son Najeriya kuma a Najeriya yake zaune da iyalansa, yasan irin abinda iyalansa ke fuskanta idan basu yi nasara ba.
Yace wasu na cewa ga mahaifiyar musa can ku zage ta. Yace dan hakane yake dagewa sosai dan kada mutane su zagi iyalansa.