Akalla Mutane 10 ne suka riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hadarin mota da ya faruwa a kauyen Bara dake karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Babu dai cikakken bayani kan hadarin zuwa yanzu. Amma wakilin Punchng ya bayyana cewa hadarin ya faru da yammacin yau, da misalin karfe 7.
Direban wata mota bas ne dake dauke da mutane, motar ta kwace masa yayi daji. Motar dai ta taso daga Kaduna ne zuwa Gombe.
Shugaban hukumar Road Safety na jihar, Yusuf Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.
A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka kama wata mata da maza 2 dakewa mutane barazanar sace su ko kuma su basu kudi
No fewer than 10 people have reportedly died in a fatal crash near Bara town in Alkaleri Local Government Area of Bauchi State.
The details of the incident are still sketchy.
Our correspondent learnt that the crash happened about 7.00pm on Sunday.
The lone crash reportedly occurred when the driver of a bus which was heading to Gombe State from Kaduna State lost control and veered off into the bush.