fbpx
Monday, August 15
Shadow

Mutane hudu sun jigata bayan da hukumar NDLEA taci karo da ‘yan kungiyar NURTW a Oshogbo

Mutane hudu sun samu rauni bayan da hukumar NDLEA da kungiyar direbobi ta NURWT sukayi musayar wuta a tsakanin su a jiya ranar alhamis.

Wannan lamarun ya faru ne da misalin karfe biyu bayan da hukumar tayi kokarin kama wani direba da take zargin dan safarar kwaya ne kuma ta tsere,

Inda tayi harbi don ta bashi tsoro amma sai ta jiwa ‘yan kungiyar NURTW hudu rauni wanda hakan yasa suka fara musayar wuta har na tsawon mintuna bakwai.

Kafin ‘yan sanda suka zo suka sasanta su, shugaban kungiyar, Kazeem ne ya bayar da wannan labarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.