fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Mutane hudu sun rasa rayukansu yayin da motar haya ta aukawa babbar akan babbar hanyar Legas-Ibadan

Mutane hudu sun rasa rayukansu sakamakon hadarin hadarin mota daya auku a jihar Ogun ranar asabar.

Hadarin ya faru ne bayan da motar haya dauke fa fashinjoji ta aukawa wata babbar mota wadda take a fake a Ogunmakin kan babbar hanyar Legas-Ibadan.

Motar hayan ta Mazda ta debo fasinjoji guda 13 ne a cikin ta, wanda suka hada da mace daya da maza guda 12.

Kuma hukumar dake lura da ababen hawa akan titi ta FRSC ta bayyana cewa macen guda tare da maza uku ne suka mutu, yayin da maza takwas ke jinya a asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published.