Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mutane miliyan ne suka rasa rayukansu a yakin Biafra domin a samu zaman lafiya a Najeriya.
Inda shugaban kasar yace bai kamata a sake barin irin wannan bala’in ya sake faruwa a wannan kasar ba wanda ya faru a shekarar 1967 zuwa 1970.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yau ranar talata yayin da shuwagabannin tsohuwar jam’iyyarsa ta CPC ta kai masa ziyara a fadarsa.
Inda yace ya kamata a hada kan Najeriya wuri guda domin a samu lafiya, kuma yana matukar godiya a garesu da kuma jinjina bisa goyon bayansa da suke yi.