fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Mutane sama da Dubu 8 aka kashe a shekarar 2021 a Najeriya

Mutum aƙalla 8,372 aka kashe a fadin Najeriya cikin shekarar 2021 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da masu iƙirarin jihadi, a cewar wani rahoto da aka fitar ranar Laraba.

Nazarin binciken ya gano cewa matsalar garkuwa da mutane ta ƙaru da kashi 58 cikin 100 daga Oktoba zuwa Disamban 2021, inda aka samu rahoton garkuwa da mutum sau 574.

Rahoton na kamfanin Beacon Consulting mai sharhi kan al’amuran tsaro, da ya yi duba kan mace-macen da aka samu sakamakon rikice-rikice kawai, ya ce an kashe mutum aƙalla 1,516 cikin wata ukun ƙarshe na shekarar 2021.

Yankin arewa maso yamma ne ke da mutum adadi mafi yawa na 3,051 da aka kashe a wata ukun, sai arewa maso gabas da yake da 1,895, da arewa ta tsakiya mai 1,684.

Yankin kudu maso gabas na da 853; kudu maso kudu na da 448, sai kuma kudu maso yamma mai 441.

Sai dai kamfanin ya ce mahangarsa ta tsaro ba ta ruwaito musu samun kisa ba daga jihohin Kano da Bauchi da Bayelsa da Ekiti da Jigawa.

Adadin na nufin kashi 79.2 cikin 100 na mutanen da aka kashe a Najeriya a arewacin ƙasar ne, in ji rahoton.

Wannan layi ne

Garkuwa da mutane

Nazarin ya nuna cewa jihohin arewa maso yamma ne kan gaba, inda aka sace mutum 3,101, sai arewa ta tsakiya mai biye mata da 1,082.

Arewa maso gabas na da 276; kudu maso kudu 245; kudu maso yamma 223; kudu maso gabas 91.

Alƙaluman sun nuna cewa jihohin arewa maso yamma ne ke da mafi girman adadi na kashi 61.8 cikin 100 na mutanen da aka yi garkuwa da su a Najeriya.

Jumilla, yankin na da kashi 88.9 cikin 100 na yawan aikata sace-sacen mutane a Najeriya ya zuwa yanzu, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Abubuwan da binciken ya yi la’akari da su

Nazarin ya mayar d hankali ne kacokam kan matsalolin da ke da alaƙa da rikice-rikice na ‘yan bindiga masu satar mutane da kuma waɗanda ke faɗa da ikon gwamnati.

  • Jihohin Arewa: Satar mutane da kashe su domin neman kuɗin fansa da ‘yan fashin daji ke yi
  • Jihohin kudu maso gabas: Tashin hankali sakamakon gwagwamyhar ƙungiyoyin da ke son kafa ƙasar Biafra
  • Arewa maso gabas: Rikicin masu iƙirarin jihadi
  • Ƙaruwar tashin hankali mai nasaba da siyasa wanda ke alaƙa da shirin jam’iyyar APC na gudanar da babban taronta na ƙasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.