An ga Jupiter da Venus, duniyoyi biyu mafi haske, wadanda suka bayyana tare da juna a sararin samaniya da safe.
Ana ganin su da ido a sassan Birtaniya da wasu kasashe da ke tsakiya da arewacin duniya, da kuma wani sashe na Amurka.
Masana sun ce duniyoyin sun kasance kusa da juna, kamar wasu taurari masu haske.
An fi ganinsu a Birtaniya, minti 40 kafin fitowar rana, amma duniyoyin suna fara bayyana ne kafin fitowar Al Fijir.
A yayin da ake iya ganinsu da ido, wasu da suka yi amfani da na’urar hangen nesa na iya ganin wasu halittun duniyar Jupiter.
Mutanen Birtaniya da dama sun yada hotunan yadda duniyoyin biyu suka bayyana a shafukan sadarwa na Intanet.
bbchausa.