Mutane tara sun mutu yayin da 12 suka samu munanan raunika samamakon hadarin mota akan babbar Kaduna zuwa Abuja.
Hadarin ya auku ne a yau ranar alhamis da misalin karfe 5 na safe sakamakon gudu a titi cewar hukumar dake lura da ababen hawa akan titi ta FRSC.
Inda suka kara da cewa hadarin ya auku ne da motoci hudu, Toyota guda biyu da kuma manyan motoci biyu.
Wanda yayi sanadiyar mutane tara kuma ya jigata mutane 12 a Rigachukun jihar Kaduna.