Hukuma ta damke wani masheki daya tsere a gidan kurkuku na Kuje da ‘ya ta’adda suka kaiwa hari ranar talata.
Oluwatosin Ikuhemeyin dan shekara 24 ya kasance dan kungiyar asiri kuma ya kashe mutane da dama wanda hakan yasa ake masa kirari da 4G Network.
Kuma dan jihar Ondo ne, yayin da aka kama shi a cikin bayi inda aka mayar dashi gidan yarin na Kuje.
Sai dai yace shi mutane uku kadai ya kashe ba kamar yadda hukuma ke cewa ya kashewa mutane marasa adadi ba.