Jiya Larabane aka tuna da rushe wani masallaci me tarihi da ake kira da masallacin Babri dake kasar India, wanda mabiya addinin Hindu suka taru suka rusashi a shekarar 1992, shekaru 25 da suka gabata kenan.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Dalilin rusa wannan masallacin shine, mabiya addinin Hindun, sunyi zargin musulmai da gina masallacin akan gurin da dakin bautarsu yake, wanda daya daga cikin manyan allolinsu da ake kira Rama, ke ajiye a ciki.
Wakilin bbc dake kawo musu rahoto daga kasar Indiya a wancan lokaci, ya shaida faruwar abin, ya bayar da labarin cewa mabiya addinin Hindu su dubu goma sha biyar suka tunkari masallacin, suka kutsa tsakanin jami’an tsaro da sukawa masallacin shinge, suka rushehi, ko bulo daya basu bariba.
Wakilin bbcn ya kara da cewa shugaban ‘yansandan dake aikin kare masallacin, ya rika tura ‘yan uwanshi ‘yan sanda domin samun hanyar guduwa, saboda ruwan duwatsun da mabiya addinin Hindun auka rika musu.
Bayan rusa masallacin an samu zanga-zanga mafi muni a kasar Indiya wadda rabon da aga irinta tun lokacin da aka bayar da ‘yancin kan kasar, haka kuma an samu asarar rayuka kimanin dubi daya.
To saidai wani ikon Allah da abin farinciki shine, uku daga cikin manyan shuwagabannin da suka jagoranci wancan aikin na rusa masallacin Babri, duk sun musulunta, kamar yanda shafin gidan talabijin na Samaa ya ruwaito.
Samaa tace mutane uku da akewa kallon jarumai a garuruwansu, saboda jagorantar rusa masallacin Babri da sukayi, Allah ya kimsa musu shiriya, sun musulunta.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Daya daga cikinsu da ake kira da balbir singh, shugabane a wata kungiyar mabiya addinin hindun kuma shine ya hau kan Hasumiyar masallacin Babri, lokacin da ake rushehi, yanzu ya zama musulmi kuma ana kiranshi da sunan Muhammad Amir. shi wannan Muhammad Amir tare da wani shima wanda yana cikin aikin rusa masallacin amma yanzu ya musulunta da ake kira da suna Muhammad Umar, sunyi alkawarin gyara ko kuma gina masallatai dari dan su wanke zunubinsu na rushe masallacin Babri.
Yanda akai Balbir Singh ya karbi addinin musulunci shine, yaje kashe wani limami da ake kira da Kaleem, sai ya iskeshi yana huduba, ya jirashi ya gama huduba, a lokaci guda kuma yana sauraron abinda limamin ke huduba akai, cikin ikon Allah hudubar tasa zuciyarshi tayi sanyi, yaji yana son shiga addinin musulunci, haka ya tunkari limamin, ya bayyanamishi burinshi kuma yayi kalmar shahada, yanzu dai ya bar garinsu inda mafiyawanci mabiya addinin Hindune, ya koma wani garin, ya auri musulma kuma ya bude makarantar isilamiya.
Na ukunsu kuwa shine Shiv Prasad, shima ya taka rawar gani wajan rushe masallacin babri, Shine ahugaban matasan wata kungiyar addinin Hindu, kuma yana da matasa da dama da yake baiwa horo.
Bayan rushe masallacin Babri, wani ciwo me kama da na hauka ya kamashi, ya rika gani da jina abubuwa shi kadai, ba tare da suna faruwa a zahiri ba, yaje ya nemi magani a guein wani limaminsu na addinin Hindu, haka kuma an kaishi asinitin mahaukata, amma duk bai samu saukiba, daga karshe ya ware kanshi daga cikin mutane na kusan shekaru biyar, ya samu sauki.
Ya bar kasar Indiya, yaje kasar hadaddiyar daular larabawa cirani, a canne Allah ya haskaka zuciyarshi ya amshi addinin musulunci, ya kuma zabi sunan Muhammad Mustafa, da ‘yan uwanshi suka ji labarin ya amshi musulunci, sai suka aikamai da sakon cewa, sun cireshi daga cikinsu kuma idan ya sake ya dawo kasar Indiya, zai dandana kudarshi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});