fbpx
Monday, August 15
Shadow

Mutanen da aka ga Sojoji sun kama a Kaduna ba ‘yan Bindiga bane, Kuskure aka yi, Makiyayane da ba ruwansu>>’Yansanda

Hukumar ‘yansandan jihar Kaduna ta bayyana cewa, bidiyon da ya yadu sosai a shafukan sada zumunta da ya nuna sojoji na saka wasu mutane a mota da sunan ‘yan Bindiga, kuskurene.

 

Tace mutanen Makiyayane wanda basu da alaka da ayyukan ta’addanci.

 

Duka sojoji da ‘yansanda sun bayyana cewa mutanen Makiyayane da suka je Kakura a karamar hukumar Chukun ta jihar Kaduna inda ‘yan Bijilante suka kamasu su da sunan cewa ‘yan Bindiga ne.

 

Kwamishina ‘yansandan jihar Kaduna yace abinda ya faru shine wasu ‘yan Bindiga sun kaiwa garin Kakura hari inda kuma suka kaiwa wata rugar Fulani hari suka sace musu shanu.

Karanta wannan  Labari me dadi: 'Yan bindiga sun sako mutane 35 da sukayi garkuwa dasu a Millennium City dake jihar Kaduna

 

Mutanen Kakura sun shiga daji dan farautar wanda suka kai musu hari yayin da suma Fulanin da aka sacewa shanu suka bi sahun barayin, anan ne aka hadu sai aka kashe Fulani 3 da jikkata wasu.

 

Yace shine sojoji suka je suka kama wadannan Fulani sannan kuma suka kai wanda aka jikkata Asibitin 44 na sojoji dake Kaduna.

 

Yace sun zauna da bangaren Fulanin da mutanen garin Kakura inda suka fahimci hakan, yace an baiwa kowane bangare shawarar aje a yi sulhu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.