Malam Tukur Mamu wanda ya taimaka gwamnati wurin sasantawa da ‘yan bindiga suka saki mutane 11 cikin wa’yanda su kayi garkuwa a harin jirgin kasa na Kaduna yace sauran mutanen dake dajin ka iya mutuwa.
Ya bayyana hakan ne saboda macizai na cizonsu kuma ba wata cikakkiyar kulawa suke samu ba, kuma yace nan yan makonni zasu iya rasa rayukansu saboda rashin lafiya.
Mamu wanda ya kasance hadimin Sheki Ahmad Gumi ya shawarci gwamnatin tarayya ta tashe tsaye ta gaggauta ceto sauran mutanen dake hannun ‘yan bindiga a dajin.
Amma yace shi ya gama nashi aikin ba zai sake shiga wannan lanarin ba saboda tsaro.