fbpx
Friday, July 1
Shadow

Mutanen da suka ‘kashe mace mai zaman kanta’ saboda Kur’ani sun gurfana a kotu

Rundunar ƴan sandan Jihar Legas ta gurfanar da mutum uku a gaban kotu bisa zargin su da lakada wa mata mai zaman kanta, mai suna Hannatu Salihu duka har sai da ta mutu.

Waɗanda ake zargin sun kashe Hannatu tare da ƙona gawarta saboda zargin ajiye Kur’ani mai tsarki a karkashin filo da ke ckin ɗakinta.

Waɗanda aka gurfanar ɗin dai sun haɗa da Abubakar Musa da Sarauta Monsur da kuma Sirajo Yusuf.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai.

Karanta wannan  Gwamnoni da ministocin arewa maso yamma sun gudanar da taro sun bukaci Tinubu ya zabi abokin takararsa a yankin su

Ya ce, tuni aka gabatar da batun ga sashin binciken manyan laifuka na jihar, kuma an gurfanar da mutanen uku a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.