fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Mutanen garuruwan dake tsakanin Kaduna da Abuja na rokon Gwamna El-Rufai kada ya tashesu daga garuruwansu

Mutanen garuruwa 3 dake tsakanin Kaduna zuwa Abuja, Akilibu, Rijana, da Katari sun roki gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da kada ya tayar dasu daga garuruwan nasu.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa, Gwamna El-Rufai ya zargi wadannan garuruwa da baiwa ‘yan Bindiga mafaka da kuma bayanan sirri wanda hakan ke taimaka musu kaiwa matafiya hare-hare.

 

Saidai Shuwagabannin wadannan garuruwan sunce basu san da mutanen garinsu dake baiwa ‘yan Bindigar bayanan sirri ba.

 

Dan haka suka roki gwamnan da kada ya tashesu daga inda suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published.