Rahotanni daga inda aka kaiwa tawagar motocin shugaba Buhari hari a kusa da garin Dutsinma sun bayyana cewa, tawagar ta shugaba Buhari bata yi musayar wuta da ‘yan Bindigar ba.
Mutanen kauyen sun bayyana cewa, sai bayan da ‘yan Bindigar suka wucene sannan kuma tawagar shugaban kasar ta wuce tana harbi a iska.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, ana zargin ‘yan Bindigar da suka kashe mataimakin kwamishinan ‘yansanda ne suka kai wannan hari.