fbpx
Monday, June 27
Shadow

Mutum 30 sun bata bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a Rann

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mutane 30 sun bata, bayan wani hari da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai a ranakun karshen mako.

Ganau sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Rann, lokacin da wasu mazauna garin suka tafi yin itace kuma maharan sun zo ne a kan babura.

Wadanda suka tsere wa harin sun jikkata, yayin da ake fargabar maharan sun sace gwamman mutane.

Kawo yanzu babu tabbacin wadanda suka kai harin, sai dai dukkan mayakan Boko Haram da kungiyar IS na kai hare-hare a yankin.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Gwmamna Uzodimma ya gargadi 'yan bingar jihar Imo su bar jihar nan da kwanaki goma kafin zuwan shugaba Buhari

Jami’an tsaron Najeriyar ba su ce uffan ba kan wannan harin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.