fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Mutum 32 ‘yan Iswap suka kashe a Kala-balge a Borno

Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta yi karin haske game da kisan farar hular da mayakan Boko Haram da ISWAP suka yi a kauyen Mudu, mai nisan kilomita 45 daga garin Rann, shalkwatar karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar a ranakun karshen mako.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, Malam Isa Gusau, shi ne ya tabbatar wa manema labarai a ranar Laraba, a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta tabbatar da jikkatar mutane shida, yayin da wasu biyu kuma suka tserewa harin ba tare ko ƙwarzane ba.

“Gwamna Babagana Umara Zulum ya damu matuka kan abin da ya faru na kashe farar hular da aka yi a ranakun karshen mako.

“Gwamna Zulum ya tattauna da shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan jihar Borno, Mohammed Dige, mai wakiltar Kala-Balge mazabar da mutanen suka fito”, in ji Gusau.

Karanta wannan  Dattawan Arewa sun gargadi Atiku cewa kar ya canja Okowa a matsayin abokin takararsa

Sanarwar ta kara da cewa daga bayanan da ya samu daga bakin ɗan majalisar, an tabbatar da matasa 32 ne ‘yan bindigar suka kashe ba sama da 40 kamar yadda rahotanni ke cewa.

Sannan ba manoma ba ne kamar dai yadda batun ke ta yawo a kafafen yada labarai, kuma sun ƙware ne a fannin kasuwancin karafa. Kuma sun niƙi gari har zuwa ƙauyen Mudu da ke karamar hukumar Dikwa domin samun ƙarafa.

Isa Gusau ya kara da cewa, a ranar Talata ne tawagar sojoji da shugaban karamar hukumar Kala-Balge suka gano gawar mutane 14, wadanda alamu suka nuna an daure su kafin a harbe su da bindiga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.