fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Mutum 50,000 a Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa kasar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga

Mutum 50,000 a Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa kasar Nijar sakamakon hare-haren yan bindig

Sama da mutane 50,000 a garuruwa 17 dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa jamhuriyyar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltan mazabar Sabon Birni ta Arewa, Aminu Almustapha Boza, ya bayyana hakan, rahoton DailyTrust.

Boza yace yanzu haka mutan wadannan kauyuka suna neman mafaka a kauyen Tudun Sunnah, dake karamar hukumar Gidan Runji, jihar Maradi a jamhuriyyar Nijar.

Dan majalisan ya kara da cewa ya dade yana kokarin ganin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan lamarin amma abin ya ci tura.

Yace Na dade ina kokarin ganin gwamnan amma ya hana ni ganinsa saboda ya san dalilin da yasa nike son ganinsa.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

“Ana kashe mutanenmu kullum. Kawo yanzu, mun kirga sama da mutum 50,000 da sukayi gudun Hijra jamhuriyyar Nijar. Sai da muka kwashe kwanaki biyu muna kidayarsu gaban gwamnan Maradi da shugaban karamar hukumar Gidan Runji.

Na yi nadamar shiga siyasa. Na san irin gudunmuwar da muka baiwa gwamnan a karo na biyu saboda ya yi alkawarin bamu tsaro da cigaba, amma kalli mutanenmu yanzu, suna shan wahala kuma ko zuwa bai iya yi ko kuma ya turo wakilai ko akalla kayan tallafi.

“Lokacin karshe da ya zo garin shine lokacin da yan bindiga suka kashe mutane a Tarah bara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.