Mutane bakwai da ke tafiya don jana’izar mamaci sun mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kan titin Ogidi-Abatete a karamar hukumar Idemili ta jihar Anambra.
Wasu mutane da dama dake tafiya tare da mamatan sun samu raunika dayawa.
Hadarin, wanda ya faru da misalin karfe 5.15 na daren ranar Juma’a, ya shafi wata motar daukar yashi da kuma wata motar bas dauke da mutane 19.
An ce bas din na dauke da iyale ne wanda ke hanyar zuwa bikin binne yan uwansu alokacin da suka hade da motar daukan yashin.
Wani shaidar gani da ido ya ce, “Mutane bakwai ne suka mutu a wannan wurin yayin da wasu fasinjoji suka samu raunuka.
“Yawancinsu yan gida daya ne wanda ke hanyar zuwa wurin jana’izar.”
Jami’in sashen kula da lamuran jama’a na hukumar kula da lafiya ta kan titi na tarayya(FRSC), Pascal Anigbo ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu.
Ya ce an ajiye gawawwakin a asibiti, yayin da wadanda suka ji rauni suna karbar magani.