Rahotanni daga jihar Legas sun bayyana cewa mutum na 3 da hadarin jirgin sama da ya fada a Opebi dake jihar ya mutu.
A baya dai an ruwaito cewa mutane 2 ne suka mutu nan take inda aka garzaya dana 3 din Asibiti magashiyan, shima dai ya mutu bayan fama da jinya.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, LASEMA ta tabbatar da wannan lamari.