Abdullahi, dan Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a matsayin mutumin kirki da mutane suka taru suka rusa.
Abdullahi ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuli, yayin da yake maida martani ga Sanata Shehu Sani inda ya bayyana yadda Jonathan a matsayin wanda ya sadaukar da son rai, bangaranci na siyasa, addini da kabilanci domin samun zaman lafiya da hadin kan kasar.
Abdullahi ya rubuta;
“Mutumin kirki wanda duk kuka taru kuka wargaza saboda mummunar adawa ta siyasa. Gashi yanzu dukkanku kun dawo kuna kuka.”