fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Mutun guda ya mutu, dayawa sun jigata bayan da ‘yan sanda suka budewa ‘yan Shi’a wuta yayin da suka fito zagaye a jihar Kaduna

Mutun ya mutu yayin da dayawa suka jigata bayan hukumar ‘yan sanda sun budewa ‘yan Shi’a wuta a Zaria, jihar Kaduna yayin da suke gudanar da zagayen su na ranar Qudus.

‘Yan shi’ar suna gudanar da wannan zagayen ne a kowace shekara a juma’ar karshe ta watan Ramadan.

Kuma an sami labari cewa suna tsaka da zagayen nasu ne hukumar ‘yan sanda ta bude masu wuta wanda hakan yayi sanadiyyar rayuwar mutun guda, wasu kuma da yawa suna asibiti rai na hannun Allah domin sunji rauni da bulet na bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.