Hukumar kula da ababen hawa da kiyaye haddura ta FRSC ta ce mutane 2 ne suka mutu yayin da wasu 6 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya faru a Asukuya kan hanyar Gboko-Makurdi a ranar Asabar.
Kwamandan Hukumar FRSC reshen Jihar Benuwe, Mista Aliyu Baba, ya shaida wa manema labarai cewa mutane 10 ne hatsarin ya rutsa da su.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan tayar motar bas din ta fashe, wanda hakan ya sa direban ya rasa yadda zai yi.
Baba ya ce wadanda suka samu raunuka an kaisu wani asibiti da ke kusa da su domin kula da su.
Baba ya kuma shawarci masu amfani da hanya da su kasance masu lura yayin tuki a ko da yaushe kuma su bi dukkan dokokin da ka’idojin tuki