fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Mutuwar Fadila(Lollipop) Allah ne ya karbi Addu’arta>>Cewar Mahaifin Marigayiyar

Rahotanni sun bayyana cewa ciwon zuciyane yayi silar rasuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Fadila Muhammad da aka fi sani da Lollipop.

 

A ranar Juma’a 28 ga watan Augusta ne da misalin Karfe 11 na darene Lollipop ta rasu a cikin motar Mahaifinta tana da shekaru 27, kamar yanda hutudole ya samo muku daga Mujallar Fim.

 

Dama tana fama da ciwon Zuciya wanda kuma a ranar shine yayi mata tasowar Karshe, ta rasu a motar mahaifinta yayin da yake hanyar kaita Asibiti.

 

A hirar da yayi da majiyar tamu, Malam Muhammad ya ce, “Wannan rashi da mu ka yi babu abin da zan ce sai Allah ya jiƙan ta da rahama, Allah ya sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare ta” Ya na faɗin haka sai ya fara kuka.

Ya ci gaba da cewa: “Wannan yarinya babu abin da zan ce mata sai Allah ya saka mata da alheri, Allah ya yi mata sakayya da gidan Aljanna.
“Yadda wannan yarinya ke yi min biyayya, Allah na gode maka da ka amshi ran wannan yarinya a hannu na!”
Ya ci gaba da faɗa wa wakilin mu cewa: “Kai dai ganau ne, tun daga  gida zuwa gidan ta na gaskiya ka ga irin ɗan’adam da su ka halarci jana’izar ta.
“Kuma rasuwar yarinyar nan, in da Allah ya ƙadarta sanadiyyar wani abu ne na ɓacin rai, ka ga mutum ba zai damu ba; za ka ga ka haifi yaro, in ya mutu ba ka damu ba ko kuma ka ce gara a kashe shi ma. Amma ka ga ‘yan’uwa da abokan arziki da iyaye kowa na zub da hawaye. Na san dai wannan yarinya Alhamdu lillahi!
“Kuma kullum addu’ar ta Allah ya karɓi rayuwar ta kafin nawa, don ba ta son ni in rasu in bar ta.
“Abin da zan rinƙa tunawa game da ita, a kullum burin ta me za ta yi min da zai sa na samu sauƙin rayuwa.”
A game da maganar su ta ƙarshe da Fadila, Malam Muhammad ya ce: “Jiya na ɗauke ta zan kai ta asibiti, ta ce min, ‘Baba ka yi haƙuri, na ga ka na ta wahala da ni.’ Sai na ce mata, ‘Ai ba siya ki ka yi a kasuwa ba, fata na dai Allah ya sa mu yi ƙarshe mai kyau daga ni har ke.’ Wannan abu ba zan taɓa mantawa da shi ba!”
A nan ma sai shauƙi ya fizge shi, ya shiga kuka.
Daga baya, sai dattijon ya iske wakilin mujallar Fim a inda ya ke tsaye, ya ba shi saƙo zuwa ga ‘yan fim duka, ya ce: “Ku ke hulɗa da ‘yan fim ɗin nan da sauran jama’a. Don Allah ku taimake ni ku faɗa wa mutane in da wanda ke da wani alƙawari na bashi tsakanin shi da Ummi, don Allah kada ya yi ƙasa a gwiwa, ya zo har gida na ya sanar da ni.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Hukumar 'yan sandan kasar Tamzania ta sako shahararren mawakin Najeriya Kizz Daniel bayan ta kama shi

Leave a Reply

Your email address will not be published.