fbpx
Friday, July 1
Shadow

“Muyi addu’a Allah ya bamu shuwagabanni na gari mu daina nuna qabilanci da banbancin addini”>>Gwamna Uzodinma

Jam’iyyar APC ta tsayar da Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa, amma zabar mataimakinsa na nema ya tada zaune tsaya.

Inda Tinubu ke shirun zabar dan uwansa Musulmi amma kungiyoyin Kirista da masu hannu da tsaki a jam’iyyar sunki amincewa da hakan.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC yau a babban birnin tarayya Abuja, Inda gwamnan jihar Imo Uzodinma yace a kundin tsarin mulkin Najeriya babu inda aka ce dole a zabi Musulmi da Kirista,

Saboda haka abinda ya kamata mutane suyi shine addu’a cewa Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi abar wata maganar qabilanci da banbancin addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published.