Wani abin ban mamaki ya faru a siyasar kasarnan wanda a tarihi mudai bamu tabajin wani dan siyasa da yayi hakan ba. Dan majalisar wakilai me wakiltar mazabar Shiroro, Rafi, Munya dake jihar Naija, Abubakar Chika Adamu ya rubuta wasika inda ya bayyana cewa an zabeshi a matsayin dan majalisa amma yanzu tunda zabe ya matso to yana gayawa Duniya cewa shi baya bukatar sake tsayawa neman takarar kujerar da yake kai, dalilinshi kuwa shine maganar Manzon Allah (S.A.W) da yace duk wanda ya nuna kwadayin mulki to be cancanci a bashi mulkin ba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ya kara da cewa irin yanda mutanen kasarnan basu yarda da yanda ‘yan majalisar ke gudanar da ayyukansu ba to indai ba son rai zai saka ba shi bega dalilin da zaisa yace sai ya sake neman tsayawa takaraba.
Ya kuma godewa Jam’iyyarshi ta APC da ta zabeshi a matsayin wanda ya cancanta ya tsaya mata takara a shekarar 2015 data gabata.
A karshe ya jawo hankalin jam’iyyar ta APC a jihar Naija can cewa akwaifa matsala tsakanin masu rike da mukaman siyasa a jihar domin babu hadin kai da aiki tare dan cigaban al’umma yanda ya kamata kowa aljihunshi kawai yake gyarawa.
Abubakar yace a koda yaushe a shirye yake ya bayar da gudummuwa dan cigaban jam’iyyar tashi idan bukatar hakan ta taso.
Duk da wasu sun bayyana wannan wasika da wannan dan tahaliki ya rubuta da cewa wai ba dan Allah ya rubutataba, wai akwai wani dalili ya be gayawa mutane ba daya sashi yace bazai tsaya takaraba amma mudai abinda ya bayya shi zamu yadda dashi har sai idan wani abu akasin hakan ya bayyana kuma muna mai fatan Alheri.
Idan da mutanen wannan mazaba taahi zasu gane to a gaskiya basu da wanda ya dace su sake zaba sai wannan bawan Allah, idan da halima su sakashi a mukamin da yafi wannan domin kuwa samun irinshi a cikin ‘yan siyasarmu na yanzu sai an tona.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});