fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Na ba sojoji isassun kudi da makamai dan su gama da ‘yan Bindiga>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da isassun kudi da makamai ga sojojin Najeriya dan su gama da ‘yan Bindiga.

 

Shugaban yace duk wani abu da sojojin Najeriya ke tambaya da zai taimaka musu wajan aiki, baya nawa, da gaggawa yake basu shi.

 

Ya kuma yi kira ga malamai da sarakunan gargajiya su tallafa dan kawo karshen matsalar.

 

Shagaban ya bayyana hakane a yayin shan ruwa da sarakunan gargajiya da kuma malamai da ya shirya a fadarsa, jiya Alhamis.

 

Shugaba Buhari yace babu gwamnatin data baiwa bangaren tsaro muhimmanci a tarihin Najeriya kamar gwamnatinsa.

 

Yace amma matsalar tsaro matsalace data karade Duniya baki daya, dan haka ana bukatar hadaka daga dukkan masu ruwa da tsaki cikin al’umma dan magance matsalar.

Karanta wannan  Kalli gidan da iyayen Deborah suke a da da kuma wanda aka basu yanzu

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito shugaba Buhari na cewa, yace samun bayanan sirri na da muhimmanci sosai wajan gamawa da ‘yan Bindigar, yace su kuma masu taimakawa ‘yan Bindigar su sani suna taimakawa ana lalata garinsu ne.

 

Shugaban yace, sarakunan gargajiya da malamai na da rawar da zasu taka wajan samar da bayanan sirri akan ‘yan Bindigar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.