fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Na ci amanar ‘yan Najeriya idan ban tsaya takarar shugaban kasa ba>>Osinbajo

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce ya ci amanar kasa idan bai tsaya takarar mukamin shugaba kasa ba a shekarar 2023.

Mista Osinbajo ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai jihar Ondo, kuma ya gana da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC.

Ya kuma ce rike mukamin mukaddashin shugaban kasa da ya yi a wasu lokuta ya ba shi kwarewar da yake bukata domin ya jagoranci Najeriya.

“Mutane na mutuwa a kowace rana, saboda haka zai kasance cin amanar kasa idan na yi ritaya kuma na koma Legas ko Ikenne bayan wa’adin mulkinmu. Ban yi wa kasar nan adalci ba,” in ji Osinbajo.

Karanta wannan  WATA SABUWA: Buhari ya saka hannu kan dokar da ta tanadi: A rika cire haraji a cikin kudin kiran waya domin tarawa a rika biyawa nakasassu kudin asibiti

A nasa bangaren, Gwamna Akeredolu ya ce duk da cewa ‘yan deleget na jihar suna son sa kuma suna mutunta shi, ubangiji ne kawai ke bayar da mulki.

Osinbajo ya sanar da aniyarsa ta neman mukamin shugaban Najeriya a ranar 11 ga watan Afrilu, kuma tun ranar yake kai ziyara sassan kasar yana neman goyon bayan ‘yan kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.