Friday, July 12
Shadow

Na fice daga Kannywood har karshen duniya kuma naji dadin hakan>>Abdul Sahir

Jarumi kuma mawaki Abdul sahir wanda akafi sani da Mallam Ali na kwana casa’in ya ce ya fita daga masana’antar kannywood daga yau alhamis 30-05-2024, yace yayi hakan ne don samar wa kansa nutsuwa.

Idan zaku iya tunawa hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar kano karkashin jagorancin Abba elmustapha ta dakatar dashi daga shiga fina-finan hausa tsawon shekaru 2, sakamakon wani vidiyon da jarumin ya saka, wanda hukumar ke ganin ya sabawa doka da tarbiyyar jihar kano.

Mallam Ali na kwana casa’in ya fice daga kannywood, shin ko waye zai maye gurbinsa acikin kwana casa’in?

Karanta Wannan  Ba zata fashe ba>>Nazir Sarkin Waka ya kara tsokanar 'Yan Crypto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *