fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Na hango cewa Jirgin shugaban kaza zai yi hadari>>Fasto Elijah

Faston nan da ya saba cewa ya hango abubuwa zasu faru a kasarnan watau, Elijah Ayodele ya bayyana cewa, ya hango jirgin shugaban kasa zai yi hadari.

 

Ya bayana cewa kuma ya hango za’a kaiwa sansanin sojoji hari a kasashen Najeriya da Mali da Kamaru da sauransu, inda yace ya kamata ‘yan kasar su yi hankali.

 

Yace jam’iyyar PDP ma zata fuskanci rikici.

 

Yace matsalolin tattalin arziki zasu ci gaba da wanzuwa kuma gwamnatin shugaba Buhari ba zata iya magance matsalolin da ake fama dasu ba, kamar yanda Daily post ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published.