Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyya ga kasar Afrika ta kudu inda yace ya kadu sosai da faruwar lamarin.
Shugaban ya bayyana hakane a ranar Juma’a inda yace wanan ambaliyar ruwa irintace mafi muni a ‘yan kwanakinnan.
Ambaliyar ruwan ta kashe mutane 341 inda wasu suka jikkata.
Shugaban yayi kira ga Shuwagabannin nahiyar Afrika dasu baiwa hukumomin agaji muhimmanci saboda shiryawa faruwar annoba irin ambaliyar ruwa.