Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya kadu sosai da fashewar gas din data faru a jihar Kano.
Shugaban ya bayyana hakane akan fashewar gas din data faru a Unguwar Sharada dake Kano inda mutane da dama suka jikkata.
Shugaban a sanarwar da ya fitar ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, jami’an lafiya dana agaji suna aiki tukuru wajan ganin sun baiwa wadanda lamarin ya rutsa dasu kulawar data kamata.