Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe sama da naira biliyan dari wurin yin tituna a jihar cikin shekaru biyu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a karshen makon daya gabata yayin daya ke ganawa da shuwagabannin gargajiya na kananun hukumomi 27 dake jihar.
Inda ya kara da cewa ko gwamnatinsa bata da wa’yan nan makudan kukaden da aka gina titunan dasu a asusunta.
Amma dangantakarsa da shugaba Buhari da kuma kasancewar su a jam’iyya guda ce tasa gwamnatin tarayya ta mara masa yayi wannan aikin.