fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Na kusa da Buhari na ta kokarin ganin Tsohon Shugaban kasa, Jonathan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a APC

Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ke kusa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari na ta kokarin ganin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya samu takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar APC.

 

A baya dai an ji cewa Goodluck Jonathan ya gana da dan uwan Buhari, Mamman Daura, saidai wata majiya tace mamman Daura ne ya je gidan Goodluck Jonathan.

 

Hakanan shima shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya gana da Jonathan kamar yanda majiyar ta ruwaito.

 

Wasu daga Arewa dai sun saiwa Goodluck Jonathan fom din takarar APC kamar yanda Rahotanni suka nuna amma daga baya wata majiya tace Jonathan ne ya baiwa gwamnan jihar Jigawa kudi ya sai masa fom din ta bayan fage.

Leave a Reply

Your email address will not be published.