fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Na kusa yin ritaya bayan cutar korona ta kama budurwa ta>>Edinson Cavani

Edinson Cavani ya koma kungiyar Manchester United ranar litinin a kyauta da kwantirakin shekara daya tare da zabin kara wata shekara a kungiyar Premier League din, wadda ya bayyana cewa ta kasance daya daga cikin mayan kungiyoyin duniyar wasan kwallon kafa.

Dan wasan mai shekaru 33 zai samu albashin yuro miliyan 11 a kowace shekara daga United tare da karin yuro miliyan 2 sai kuma karin wasu yuro miliyan 4 na siyen shi da suka yi. Cavani ya kasance tsohon dan wasan PSG wadda ya bari a karshen kakar data gabata bayan dauki tsawon shekaru 7 a kungiyar.

Kuma dan wasan ya samu kwantiraki daga wasu kungiyoyi amma ya fara tunanin yin ritaya saboda annobar korona ta fara shafar iyalan shi. Cavani ya bayyana cewa “A koda yaushe lafiyar iyalai ce a sahun farko, mun sha fama da cutar korona tare da iyalai na da budurwata kuma har na fara tunanin yin ritaya daga wasan kwallon kafa domin na cigaba da zama a kasa ta”.

Karanta wannan  Manchester United ta ragewa Ronaldo albashi bayan yace zai sauya sheka a wannan kakar

Dan wasan ya kara da cewa”Cutar korona tanada azaba sosai tare da kuma ban tsoro amma yanzu mun gode Allah saboda gabadaya mun warke daga cutar”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.