Matashin mai suna Abdulmuhyi Bagel Garba, wanda kani ne ga kwamishinan wutar lantarki da kimiyya da fasaha na Jihar Bauchi, Hon Garba Bagel, ya wallafa hakan ne a shafinsa na kafar sada zumunta taba zuciya bayan watanni biyar da rasuwar budurwarsa.
Idan za a iya tunawa Hauwa Abdullahi Shehu, wadda take dalibar aji uku a jami’ar Jihar Bauchi, Gadau ta rasu sakamakon hadarin motar da ta yi ana saura wata daya a yi aurensu.