Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya taba yin aikin gadi amma ilimi me kyau ya canja rayuwarsa.
Ya bayyana hakane ga ‘yan Najeriya dake zaune a kasar Indiya yayin ganawarsu.
Shugaba Tinubu ya je kasar Indiya inda ya halarci taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a Duniya da ake cewa G-20.
Tinubu yace ilimi me kyau da ya samu je ya bashi damar zama shugaban kasa a yanzu.
Tinubu ya basu kwarin gwiwa inda yace zasu iya kaiwa kololuwar nasara idan suka dage akan abinda suke.
Tinubu ya bayar da labarin yanda yayi aiki a matsayin babban akawu kamin daga bisa ya bar aikin ya koma siyasa.