Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yayiwa Najariya iya bakin kokarinsa kuma zai sauka mulki yana farin ciki.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu a yayin hirar da aka yi dashi a Channels TV.
Garba yace shugaban da zai karbi mulki zai ci gaba da gina Najariya a inda shugaba Buhari ya tsaya.